Gobarar daji ta hallaka mutane 11 a Spain
July 10, 2026
Talla
Nahiyar Turai ta kasance mafi saurin dumama a duniya inda yanayin zafin ya rubanya fiye da sauran yankuna na duniya tun bayan zafin da aka fuskanta a shekarun 1980 a cewar cibiyar nazarin kimiyar muhalli ta nahiyar turai, inda ta yi kashedin cewa sauyin yanayi na daga cikin dalilan karuwar zafin sakamakon kona makamashi masu fidda hayaki kamar man fetur da kwal.
A baya gobarar daji ta yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane a tarayyar Turai inda a kasar Girka mutane fiye da 100 suka mutu a shekarar 2018.