Gomman bakin haure sun nutse a ruwan Italiya
January 1, 2025Rahotanni daga Tsibirin Lampedusa na kasar Italiya sun yi nuni da cewa, kimanin bakin haure bakwai ne aka ceto yayin da wasu 20 suka yi batan dabo, sakamakon nutsewar da kwale-kwalensuya yi a teku a kan hanyarsu ta zuwa Italiya daga Libiya. A cewar magajin garin tsibirin na Lampedusa, Filippo Mannino daga cikin wadanda aka ceto, har da wani yaro dan asalin Siriya mai shekaru takwas, wanda ke fatan ya hadu da mahaifinsa da ke zaune a nan Jamus. Sai dai kuma mahaifiyar yaron da suke tare na daga cikin wadanda suka nutse cikin ruwa.
Karin bayani: Dubban 'yan Afirka sun mutu a teku a 2024
Yin hijira daga nahiyar Afirka zuwa Turai da nufin samun rayuwa mai inganci ta ruwa na daga cikin manyan abubuwa mafi hatsari a duniya, inda alkalumma hukumar kula da kaura ta duniya suka yi nuni da cewa kimanin mutane dubu 24,500 ne suka bace ko kuma suka mutu a tsakiyar tekun Bahar rum tun daga shekarar 2014.
A yanzu haka kasar Italiya na shirin dakatar da shigar bakin haure zuwa Turai ta kasar, wanda a cewarta hakan zai rage yawan asarar rayukan da ake yi a teku.