Burkina Faso: Nakiya ta salwantar da rayuka
September 6, 2022Talla
A cikin sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar, ta ce, hatsarin ya faru ne a tsakanin garuruwan Djibo da kuma Bourzanga.
Mutanen dai sun gamu da ajalinsu ne yayin da suke kan hanyar zuwa babban birnin kasar Ouagadougou, kana yawancinsu 'yan kasuwa ne da kuma dalibai da za su koma makaranta daga hutu.
Ko a farkon watan Agustan da ya gabata, dakarun soji 15 ne suka mutu a wani harin da 'yan ta'adda suka kai a kan hanyar Dori zuwa Djibo da ke arewacin kasar.
Kasar Burkina Faso dai ta shafe tsawon shekaru 7 ta na fama da matsaloloin masu tada kayar baya wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 2000 yayin da wasu kimanin miliyan 2 suka rasa matsugunnansu.