Gomman mutane sun mutu a wani gidan rawa a India
December 7, 2025
Rahotanni sun yi nuni da cewa, mutane uku sun rasa rayukansu ne a sanadiyar mummunar rauni, yayin da wasu 20 suka ce ga garinku nan sanadin sarkewar numfashi, sakamakon hayakin da ya turnuke. Binciken farko-farko ya nuna cewa gobarar ta tashi bayan da wata tukunyar gas ta fashe a cikin kicin.
Karin bayani:Gobara ta halaka mutane da dama a Indiya
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X shugaban yankin, Pramod Sawat ya ce ya kai ziyara inda lamarin ya auku a gundumar Arpora, inda ya bayar da umurnin gudanar da bincike kan musababbin tashin gobarar. A cewarsa, za a hukunta duk wanda aka gano da yin sakacin da ya haifar da gobarar da ta lakume rayukan mutane, ciki har da wasu 'yan yawon bude ido hudu. Offishin Firanministan kasar, Narendra Modi ya ce za a biya iyalan wadanda hatsarin ya rutsa da su fiye da dala 2,000 a matsayin diyya.