Goodluck Jonathan yayi afuwa ga wasu mutane
March 13, 2013 A wani abun dake zaman kama hanyar fuskantar kace nace a cikin yakin cin hanci a Tarrayar Najeriya, shugaban kasar Goodluck Jonathan yayi gaban kansa, wajen afuwa ga tsohon gwamnan jiharsa ta Bayelsa da a baya aka kame da batun satar kuɗi a ƙasar Ingila.
Wasunsu dai ana zargin su ne da ƙoƙari na juyin mulki wasu kuma sun kai ga tabbata amsa sunan fatake na dare. To sai dai kuma daga dukkan alamu sun kai ga karatun yanci ga shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan da ya bayyana afuwa ga wasu fitattun 'yan ƙasar kusan Goma,afuwar kuma da daga dukkan alamu ke shirin barin baya da kura a cikin ƙasar, sakamakon zargin da fadar ke fuskanta na ɗaurin gindi ga ɓarayi.
Da farkon fari dai shugaban ya so fakewa ne da zaman Majalisar
Magabatan Tarrayar Nijeriya da suka zauna suka dubi jerin batutuwa da dama,wajen kaiwa ga yanke hukuncin da yanzu haka ya fara kaiwa ga martani mai nauyi.
To sai dai kuma taron ya kare a fadar gwaman Murtala Nyako na jihar
Adamawa ba tare da kaiwa ga biyan bukar shugaban kasar ba.
To sai dai kuma shugaban ya bi dare ya kai ga amincewar afuwar da ta haɗa da tsohon gwamnan jihar Bayelsa Diarieye Alaghmesia da jami'an tsaron kasar Birtaniya suka cafke da batun kokarin sace kudin kasar, sannan kuma ya wayi gari ya na ji a jikinsa sakamakon martani daga kungiyoyi na farar hula dama yan adawar ƙasar ta Najeriya.
Auwal musa Rafsanjani dai na zaman shugaban ƙungiyar "Transparency in Nigeria" dake yaki da batun cin hanci a kasar kuma a tunanin sa matakin
na Jonathan na zaman kokari na zama turu ga daukacin barayin kasar ta Nijeriya.
Bada kariya ga barayi ko kuma taimakawa 'yan uwa da abokan arzuka dai,gwamantin Nijeriya dai na ta'allaka afuwar ta Alamasiegha da kokarinsa na fafutukar zaman lafiya a yankin Niger Delta.
Zargin kuma da a cewar Alhaji Isyaku Ibrahim dake zaman wani jigon
jami'yyar CPC mai adawa a kasar ke zaman zance irin na 'yan tasha a
bangaren mahukuntan.
Sama da dallar Amurka milliyan dubu 500 ne dai aka kwashe cikin tsawon shekaru 14 na sake dawowar demokaradiyar kasar ta Nijeriya. A wani abun da ke zaman daya daga cikin wasoso mafi girma a nahiyar Afirka baki daya.
Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Yahouza Sadissou Madobi