Tilasta rigakafin corona ga ma'aikatan Google da Facebook
July 29, 2021![Symbolbild I BigTech I Social Media](https://static.dw.com/image/55951470_800.webp)
Talla
Kamfanonin guda biyu sun dauki wannan mataki ne ba tare da shawarartar juna ba, sai dai Google ya ce dokar za ta shafi ma'aikatantan da ke Amirka ne kadai a yanzu kamin daga baya a fadada dokar zuwa sauran yankuna a watanni masu zuwa.
Matakin tilasta ma'aikata allurar na zuwa ne sakamakon yaduwar sabon nau'in annobar corona mai suna Delta, sai dai Google na jan kafaka na dawo da ma'aikata aiki a ofis har zuwa tsakiyar watan Oktoba.
Amma kamfanin Apple na kan bakansa na barin ma'aikatansa ci-gaba da aiki daga gida, kuma babu niyyar tilasta su yin allurar rigakafin corona.