1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gorbachev ya taka rawa wajen sauya siyasar duniya

Suleiman Babayo MAB
August 31, 2022

Shugabannin gwamnatocin kasashen duniya na ci gaba da nuna alhinin rasuwar tsohon shugaban tsohuwar Tarayyar Soviet, marigayi Mikhail Gorbachev, da rawar da ya taka wajen kawo karshen yakin cacar-baka a duniya.

	
Michail Gorbatschow gestorben
Hoto: CNP/ABACA/picture alliance

Marigayi Mikhail Gorbachev ya kasance mutumin da ake girmamawa a kasashen duniya ganin yadda ya taimaka wajen samar da tsarin dimukaradiyya a Turai. Ana kuma girmama shi a Jamus matuka saboda rashin daukan mataki lokacin da aka rusa katangar Berlin, inda Mikhail Gorbachev ya amince Jamus ta sake hadewa lokacin da yake rike da madafun iko.

Shugaban gwamnatin Jamus Scholz ya nuna alhini game da mutuwar GorbachevHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

A game da marigayin, Olaf Scholz shugaban gwamnatin Jamus ya ce: " Ya kasance shugaba mai karfin hali da jajircewa wajen kawo sauyi, ya kawo ci-gaba wajen bunkasar dimukuradiyya a Rasha da Turai baki daya. Ya mutu a lokacin da Shugaba Vladmir Putin ya kawo rikici a Rasha da Turai baki daya, ta hanyar kai hari a makwabciyar kasa Ukraine. Wannan shi ya saka muke daukan Mikhail Gorbachev da tasiri kan ci-gaban Turai da kasarmu a 'yan shekarun da suka gabata"

Irin wannan jinjina aka samu daga bangaren Firaminista Boris Johnson mai barin gado na Birtaniya wanda yake cewa tsohon jagoran ta tsohuwar Tarayyar Soviet ya taka rawa a siyasar duniya.: Ya ce: " Mikhail Gorbachev na cikin mutanen da suka sauya duniya kuma babu tambaya zuwa makoma mai kyau."

Gorbachev ya kawo sauye-sauye da dama

Helmut Kohl da Gorbachev sun taka rawar gani wajen hadewar tarayyar JamusHoto: dpa/picture-alliance

Sauye-sauye da tsohon shugaban Tarayyar Soviet Mikhail Gorbachev ya kaddamar sun janyo yunkurin kifar da gwamnati daga masu matsanancin ra'ayin gurguzu. Josep Borrell babban jami'in kula da harkokin kasashen ketare na Kungiyar Tarayyar Turai ya tuna lokacin, yana mai cewa: "Juyin mulkin a birnin Moscow, ina tunawa da ranakun na tarihi. Mikhail Gorbachev ya kawo 'yanci ga al'umar Rasha, ya yi kokarin yin sauyi karkashin tsarin gurguzu ."

Marigayin ya samu jinjina daga Amirka zuwa kasashen yankin Asiya, inda Shugaba Joe Biden na Amirka ya ce babu wanda zai yi tunanin duniya ba tare da marigayin ba, shi kuma Firaminista Fumio Kishida na Japan yana cewa: "Ya bar babban abin da ya cimma a rayuwa a matsayin jagora wajen goyon bayan rage makaman nukiliya."

Karshen yakin cacar baka tsakanin Gorbachev da Reagan ya taimaki ChainaHoto: Dennis Paquin/REUTERS

A daya bangaren Zhao Lijian ministan harkokin wajen Chaina ya tuna da rawar marigayin ya taka kan dangantakar kasashensu: Ya ce: "Gorbachev ya ba da gudumawa kan daidaita dangantaka tsakanin Chaina da Tarayyar Soviet."

Marigayi Mikhail Gorbachev ya ajiye madafun ikon tsohuwar Tarayyar Soviet ranar 25 ga watan Disamba 1991 ranar da tsohuwar tarayyar ta rushe.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani