1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGwatemala

Guatemala: Mutane 51 sun mutu a hadarin mota

Abdullahi Tanko Bala
February 10, 2025

Hukumomi a Guatemala sun ce wata motar Safa ta kubuce wa direba inda ta zame daga kan gada ta fada cikin fadama

Hadarin motar Bus a Guatemala
Hadarin motar Bus a GuatemalaHoto: Moises Castillo/AP/dpa/picture alliance

Wata motar safa dauke da mutane 70 ta kubuce wa matukinta inda ta zame daga kan gada ta fada cikin fadama a birnin Guatemala wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 51 a cewar Jami'ai.

An kai gawarwakin mutane 36 maza da mata 15 zuwa dakin ajiyar gawa a cewar Carlos Hernandez mai magana da yawun sashen kwana-kwana.

Masu aikin ceto sun sami zakulo mutane goma da suka sami raunuka daga cikin motar Bus din, da dama daga cikin su an garzaya da su asibiti.