Tasirin rayuwar marigayi Kahlifa Isyaka Rabi'u
May 15, 2018A shekarar 1925 ne aka haifi marigayi Isyaku Rabi'u ya kuma halarci makarantar allo ta mahaifinsa, inda aka horar da shi kan Alkur'ani da Larabci a tsakanin shekarun 1936 zuwa 1942, marigayin ya tafi tafi Maiduguri domin karo ilimi. A shekarar 1949 ya kasance malamin addini mai zaman kansa, inda ya fara koyar da Larabci da Alkur'ani, marigayi Mallam Isyaku Rabi'u ya fara shiga harkar kasuwanci a farkon shekarun 1950 bayan shekaru biyu ya kafa kamfanin Isyaku Rabiu & Sons a shekarun. Shiekh Muhammad Nasir Adam shi ne babban limamin daya daga cikin masallatan juma'a da marigayin ya gina kamin rasuwarsa. "Marigayi Khalifa Isyaka Rabi'u yana taimakawa dukkanin kungiyoyin ma'aikata da na addinai, marigayin yana matukar taimakawa da shawarwari kan yadda kasa za ta ci gaba."
Guddumuwar Marigayi Sheikh Khalifa Isyaka Rabi'u
Khalifan ya yi amfani da dukiyarsa wurin taimakwa addinin musulunci, ya gina masallatai da makarantu a cikin garin Kano, marigayin ya gina wa marayu da marasa karfi gidajen zama. Marigayin ya taka rawar gani wajen gina al'umma da kuma hada kan jama'a wuri daya, a shekarar 1994 ya samu mukamin Khalifan darikar Tijjaniya a Najeriya saboda gudummawar sa. Farfesa Ibrahim Muhammed na cibiyar nazarin Alkur'ani mai gira a jami'ar Bayero ya yi tsokaci kan gudumuwar marigayin." Khalifa ya jajirce wajen yada ilimin Alkur'ani, ya gina cibiyar yada ilimin Alku'ani a cikin jami'ar Bayero da ke Kano."
Marigayin ya rasu a lokacin da ake shirin bude jami'ar da ya gina a jihar Kano, wannan dai wani manuniya ce da ke tabbatar da burinsa na samar da ilimi a tsakanin musulmi da sauran al'ummar Najeriya. Marigayi Khalifa Isyaka Rabi'u ya da shekaru 90 da haihuwa ya kuma bar mata hudu da 'ya'ya 63 da kuma jikoki da dama, marigayin ya rasu a ranar 8 ga watan Mayun shekara ta 2018 a wani asbiti a birnin Landan bayan fama da jinya.