1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gudunmawar mata a siyasa a Afirka ta Yamma

February 24, 2026

Shugabannin Afirka ta Yamma sun sabunta alkawuran da suka dauka na samar da shugabanci da za a dama da kowa tare da shigar mata da matasa cikin harkokin siyasa.

Taron ci gaban matan Afirka a Ghana
Taron ci gaban matan Afirka a GhanaHoto: Francis Kokoroko/File Photo/REUTERS

Taron da ministocin kungiyar raya ci gaban tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka suka gudanar, ya yi nazari kan ci gaban da aka samu na hadakar jinsi tare da bayyana sabbin dabarun cike gibi na wakilcin mata a harkokin mulki.

Babban abin da ya fi daukar hankali a shawarwarin shi ne daidaita wakilcin mata a Jihohi a tsakanin 2025-2035 a fadin kasashe mambobin Kungiyar. Ministar kula da jinsi, yara da zamantakewar jama'a ta Ghana, Dr. Agnes Naa Momo Lartey, ta bayyana mata a matsayin "ginshikin cigaban tattalin arziki," tana mai jaddada cewa ba za a iya samun ci gaba mai dorewa ba tare da shigar da su cikin jagoranci da yanke shawara ba. Ta yi nuni da cewa, ba wa mata damar shiga harkokin siyasa zai karfafa wannan manufa.

Yaki da cin zarafin mata a GhanaHoto: Michael Oti/DW

Gwamnatin Ghana ta ma'aikatar kula da Yara, jinsi, da kare zamantakewa ta sanar da daukar matakai don samar da damammaki daidai wa daida ga kowa ta hanyar daidaita matsalolin jinsi a harkokin ci gaban kasa.

Ministar kula da jinsi da yara ta Saliyo, Isata Mahoi, ta yaba wa masana kan gudunmawar da suka bayar yayin tattaunawar ta kwanaki biyu. Ta ce ba wai don musayar ra'ayi ne kawai aka yi ba, a'a, don sake jaddada kudurin yankin na samar da manufa ta bai daya don ciyar da harkokin mulki gaba da kuma bai wa mata damammaki a fagen siyasa

Mataimakiyar shugaban kasar Ghana Farfesa Naana Jane Opoku-Agyemang ta jaddada cewa inganta shugabancin mata ba kawai a kan adalci ba ne, amma don inganta harkokin mulki da kuma samun kyakkyawan sakamako na ci gaba.