Turkiyya: Gudunmawar Musulmi Bakar fata
October 6, 2020Talla
Wannan taron dai, ana gudanar da shi ne kai tsaye ta hanyar internet, inda ake gabatar da bayanai daga bakin masana da kuma malamai dangane da irin kokarin da bakaken fata Musulmin suka yi kuma suke kan yi a bangarori dabam-dabam na ci-gaban al'umma, daga ciki kuwa har da irin yadda Musulmi bakaken fatar suka taka rawa tare da bayar da gudunmawa wajen yada ilimin addinin Islama.
Sau tari dai a kan samu bakaken fata ne suka fi karbar addinin Musluci a cikin kasashen Turai. Babbar manufar wannan taro dai ita ce kara karfafa wa bakaken fata Musulmi gwiwa domin ci gaba da kokarin da suke yi a bangarori dabam-dabam, duk kuwa da irin matsalolin da suke fuskanta.