1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gudunmawar Rediyo a zamantakewar al'umma

Abdullahi Tanko Bala
February 13, 2018

Albarkacin zagayowar ranar Rediyo ta Duniya, ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin waiwaye kan rawar da Rediyo ke takawa ga rayuwar al'umma, jama'a sun yi tsokack kan alfanun Rediyon a garesu.

Niger DW Hörer
Hoto: DW/A. M. Amadou

A Jamhuriyar Niger al'umma musaman ma mata suna samun ci gaba a fannin wayar da kai ta hanyar kafafen yada labaru daban na na gida da na kasashen waje, A zantawar da wakiliyarmu a Gaya ta jamhuriyar Niger, Ramatu Issa Oanke wasu mata sun shaida mata cewa suna sauraron rediyo ba dare ba rana suna samun karuwa ta sanin abubuwan dake wakana a duniya musamman wadanda suka shafi rayuwar iyali da kumazamantakewa.
Rediyo dai ya kawo sauyi da dama a rayuwar al'umma musaman ga matan karkara wadanda suka ce sannu a hankali suna gane amfanin da rediyon da kuma debe musu kewa ta hanyar nishadantarwa. Hasali ma suka ce rediyo ya zama tamkar makaranta a garesu.

Yara manyan gobe suna sauraron RediyoHoto: Sydelle Willow Smith


A fannin kiwon lafiya hukumomi na yin amfani da rediyo wajen rage yawan mace macen mata da kananen yara ta hanyar wayar da kan mata a kauyuka game da mahimanci zuwa asibiti domin duba lafiyarsu yayinda suke da juna biyu da kuma bayan haihuwa lamarin da a cewar Hauwa Arzika ya kawo musu ci gaba sosai.
Ita ma da ta ke tsokaci Nana Hadiza wata ma'aikaciyar rediyo ta ce baya ga batun kiwon lafiya sauraren rediyo yana taimakawa mata a fannin zamanentakewa tsakaninsu da mazajensu da kuma sauran abokan zama.

Uwa da danta. Farin cikin uwa lafiyar jaririnta,.Hoto: DW/K. Zurutuza