1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin matasa na inganta rayuwarsu

Gazali Abdou Tasawa ZMA
February 10, 2023

Ministocin matasa na kungiyar hadin gwiwar kasashen Sahel da Sahara sun yi taro kan tsaro da inganta rayuwar matasa a Yamai.

Hoto: DW/Sylvanus Karemera

Makasudin taron dai shi ne tattaunawa kan wani shiri ko program da kungiyar ta CEN-SAD ta fito da shi na samar da ayyukan yi ga matasa ta yadda za su ba da tasu gudunmawa ga yaki da ta'addanci da kuma bunkasa ayyukan noma da kiwo,  ceto gandun daji daga mamayar hamada da kuma yaki da gurbatar muhallin kasashen yakin.

Wannan taro na kungiyar CEN-SAD mai kunshe da kasashe 25 na Afirka na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar ke cika shekaru 25 da kafuwa. Taron wanda ya samu halartar ministocin matasa daga kasashe dabam-dabam na kungiyar zai nazarin kundin wani shiri da kungiyar ta CEN-SAD ta fito da shi domin inganta rayuwar matasa ta yadda za su taka rawa yaki da jerin kalubalan da yankin yake fuskanta da kuma bayar da gudunmawa ga ci gaban kasashen yankin. Malam Briji Rafini tsohon firaministan Nijar wanda shi ne sakataren zartarwa na kungiyar ta CEN-SAD.

"Ya ce wannan shiri na matasan CEN-SAD na da burin zaburar da matasa domin su kasance a sahun gaban duk wani shiri na tabbatar da tsaro da samar da zaman lafiya da yaki da talauci da kuma ceton gandin daji a wannan yanki namu. Domin a yau matasa wadanda su ne suka fi rinjaye da kwazo da azama su ne kuma kason al'ummar da jerin kalubalan da yankin yake fuskanta  ya fi shafa kai tsaye. Su ne kuma kason al'umma wanda kungiyoyin 'yan ta'adda suka fi amfani da su. Amma wannan shi ri da muka fito da shi na da burin aiki tare da gwamnatoci da duk wasu masu burin ci gaban matasa, wajen wanzar da zaman lafiya da samar da ci gaba ga wadannan kasashe namu ta hanyar amfani da basirar da kuma himmar da Allah ya yi wa matasa".

Sabon shirin gina kasashe wanda kungiyar ta CEN-SAD ta bijiro da shi zai karkata ne a wasu fannoni guda uku room dai yadda Malam Rabiou Taro shugaban kungiyar matasan kungiyar ta CEN-SAD ya yi mana karin bayani.

Taron dai ya samu halartar wakilan kungiyoyin matasa maza da mata wadanda suka is da nufin bayar da shawarwari na yadda za aiwatar da wannan shiri na amfani da matasa domin samar da zaman lafiya da kuma ci gaban yankin na sahel da Sahara. Marie Chitou daliba a jami'ar Abdoulmoumi ta birnin Yamai na daga cikin mahalarta taron ta kuma bayyana fa'idar shi a ga matasan.

Taron kungiyar ta CEN-SAD dai ya kawo karshe da yin gyaran huska ga sabon kundin tsarin ci gaban matasan yankin na Sahel da Sahara, wanda taron majalisar ministocin zai mika ga taron shugabannin kasashen yankin a nan gaba domin samun amincewarsu kafin soma amfani da shi gadan-gadan.