1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guguwa a ƙasar Australia

March 20, 2006

Wata guguwa mai ƙarfi da aka yiwa laƙabi da Larry ta ratsa ta gabar teku dake arewa maso gabashin Australia. Guguwar wadda ke tafiya da ƙarfin kilomita 290 a cikin saá guda, ta yi awon gaba da gidaje a inda alúmomi ke zaune a yankin Cairns ta jihar Queensland. kafin baiyanar guguwar hukumomi sun kwashe dubban jamaá wadanda suka hada da yan yawon bude idanu daga yankin . Cibiyar binciken yanayin muhalli ta yi hasashen cewa guguwar na iya yin mummunan taádi a da´irar kilomita 300 a gabar tekun arewa maso gabashin garin Queensland.