Guguwa mai karfin gaske ka iya afkawa Taiwan
October 31, 2024Birane da dama a Tsibirin Taiwan sun ayyana hutu, tare da soke tashi da saukar jiragen sama da kuma rufe kasuwanni, sakamakon hasashen da ke nuna ta yiwu kasar ta iya fuskantar guguwa mafi karfi a cikin shekaru 30 da suka gabata. A kalla mutane 27 suka jikkata yayin da bishiyoyi da dama suka fadi kana aka samu rahotannin zaftarewar laka a wurare hudu, a cewar hukumar kashe gobara ta kasar.
Karin bayani: Mahaukaciyar guguwar Koinu ta sake kadawa a Taiwan
Ana sa ran guguwar mai gudun gaske da ta tunkaro ta afkawa gabashin gabar ruwan kasar, wadda ke tafe da ruwan sama mai karfi da kadawar iska kuma hakan zai shafi kusan dukannin fadin Taiwan. Ma'aikatar tsaron Taiwan ta ce dakarun soji 36,000 ne suka yi shirin ko ta kwana domin gudanar da ayyukan agaji. Kawo yanzu an kwashe mutane fiye da 1,300 daga yankunan da ke da hadarin gaske. Ana dai yawan samun iftila'in guguwa a irin wannan lokacin a duk shekara a Taiwan.