1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guguwa na barna a Mozambik

Abdul-raheem Hassan
March 18, 2022

Daruruwan gidajen mutane sun rushe sakamakon ambaliyar ruwan sama, titunan motoci sun yanke saboda tsawa da ake yawan fuskanta.

Madagaskar | Zyklon Emnati
Hoto: DEFIS_EU/REUTERS

Rahotanni daga kasar Mozambik na cewa adadin mutanen da guguwa ta halaka ya karu zuwa 53, tun bayan da gugu mai karfi ta kada a kasar tsawon mako guda.

Hukumomi a Mozambik sun tabbatar da lalacewar dubban gidajen al'umma da turakan wutar lantarki a lardin Arewa maso gabar tekun kasar, ambaliyar ta raba wasu yankunan kasar saboda yankewar tituna da dama, matakin da ke hana kai agajin gaggawa ga wadanda guguwar ta shafa.

Hukumomin kula da yanayi a kasar sun yi gargadin yuwar samun barna sakamakon guguwar mai suna "Gombe" da ke gudun kilomita 200 a cikin sa'a guda. Yanzu haka dai kasar Mozambik na a cikin yanayin damuna da ke zuwa da tsawa da guguwa mai karfi game da ruwan sama da ke haifar da ambaliya.