Guguwar Hurricane na ci gaba da barazana
August 19, 2007Mahaukaciyar guguwa da akewa lakabi da suna Hurricane Dean, tayi ajalin mutum na hudu a Dominican, a yayin da take ci gaba da nausawa izuwa Jamaica. A jiya sai da mahaukaciyyar guguwar tayi asarar rayuka uku, a tsibirin Santilushia da Matines, bayan barna mai yawan gaske da tayi. Masu nazarin yanayi na hasashen cewa , mahaukaciyar guguwar dake ratsawa ta yankin Caribiyan, ka iya kara karfi har ta kai mataki na 5, wanda kusan shine mafi hatsari. A cewar rahotanni, a yanzu haka guguwar na gudun kilomita 260 a cikin sa´a daya. Ana dai sa ran daga nan izuwa wani lokaci a yau, mahaukaciyar guguwar zata ratsa izuwa kasar Jamaica.Tuni dai al´ummar kasar suka kasance cikin shirin kota kwana. Haka suma al´umman kasashen Mexico da kudancin Amurka , tuni suka yi nisa na shirin kota kwanan jiran wannan mahaukaciyyar guguwa ta Hurricane Dean.