1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guguwar Milton ta isa gabar ruwan Florida

October 10, 2024

Guguwa mai karfi ta Milton hade da ruwa sama da iska mai karfi da ke gudun kilo mita 100 cikin sa'a guda ta isa yammacin gabar tekun Florida.

Guguwar Milton ta isa gabar ruwan Florida
Hoto: CHANDAN KHANNA/AFP

Iftila'in ya haifar da ambaliyar ruwa da kuma daukewar wutan lantarki. Shugaba Joe Biden na Amurka ya yi kira ga mazauna Florida da su mutunta dokar kwashe jama'a daga yankin, yana mai cewa ta yiwu guguwar ta Milton ta kasance iftila'i mafi muni da jihar za ta fuskanta cikin shekaru 100.

Karin bayani: Guguwa ta sa Joe Biden dage ziyararsa zuwa Jamus da Angola

Kawo yanzu dai fiye da mutane miliyan daya ne ke zaune a cikin duhu yayin da ake ci gaba da gargadin mutane kan walkiya da ma ambaliyar ruwa a yankin Tampa. Ana sa ran guguwar ta ratsa zuwa gabar tekun Florida daga Yamma zuwa Gabas yayin da take rage tasiri, sai dai har yanzu tana ci gaba da zama barazana.