1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

China ta kwashe mutane dubu 340 saboda Typhoon Noul

July 25, 2026

Mahukunta a kudancin kasar China sun kwashe sama da mutane dubu 340,000 daga gidajensu tare da dakatar da aiki da zirga-zirgar jiragen kasa, yayin da guguwar Typhoon Noul ke tunkarar lardin Guangdong.

Masu aikin ceto na kwashe mutane da suka makale a China
Masu aikin ceto na kwashe mutane da suka makale a ChinaHoto: Cao Yiming/Xinhua/IMAGO

Ana sa ran guguwar za ta afka gabar tekun tsakanin biranen Shenzhen da Haifeng da safiyar Lahadi, tana dauke da iska mai karfin kilomita 151 zuwa 173 a cikin awa guda. Hukumar hasashen yanayi ta China ta fitar da gargadi mai girma kan guguwar.

An dakatar da makarantu, kasuwanci da sufuri a wasu birane 12 na Guangdong, yayin da aka dakatar da dukkan jiragen kasa a fadin lardin.

A Hong Kong ma an bude matsugunai na wucin gadi, inda aka soke akalla jirage 49 tare da jinkirta wasu 238. Kamfanin Cathay Pacific ya sanar da soke dukkan tashin da saukar jiragensa a ranar Lahadi saboda hadarin guguwar.

Masana sun ce Typhoon Noul na da matukar hadari, kuma ta na iya haddasa ambaliyar ruwa da barna mai yawa.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW