1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guguwar Wipha ta tunkari birnin Hong Kong

July 20, 2025

A Hong Kong na kasar China, an soke harkokin sufuri sakamakon mumumunar guguwar nan ta Wipha da ta tunkari birnin.

Hoto: Huang Kuo-fang/CNA/AFP

Hukumar kula da yanayi ta China ta yi gargadin cewa guguwar ta Wipha za ta ci gaba da yin karfi yayin da ta tunkari birnin Hong Kong. Gwamnatin kasar ta ce kimanin mutane 200 ne suka isa wani matsugunni da aka tanadar musu yayin da ta samu rahotannin faduwar bishiyoyi a wasu wuraren. Tuni dai aka rufe makarantu da wuraren shakatawa.

A wani labarin kuma, an gano gawarwakin wasu mutum uku bayan da wani kwale-kwale dauke da masu yawon bude ido ya kife a gabar ruwan Vietnam. Hukumomin kasar sun ce, adadin wadanda suke riga mu gidan gaskiya a hatsarin ya kai mutum 38 a yanzu. Daga cikin wadanda suka gamu da ajalin nasu har da yara kanana guda 8. Kwale-kwalen dauke da masu yawon bude 48 da kuma ma'aikatansa biyar, ya kife ne sakamakon guguwa Wipha da ta kada a lokacin da yake shawagi a gabar ruwan.