1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guguwar Yagi ta yi ta'adi a Vietnam da China

September 7, 2024

Mahaukaciyar guguwa da ake wa lakabi da Yagi ta yi ajalin mutane biyar a Vietnam da China tare da haddasa gagarumin ta'adi, sannan kuma tana ci gaba da kadawa zuwa wasu yankunan Asiya.

Asien -  Typhoon Yagi
Hoto: CNS/AFP

Akalla rayukan mutane uku sun salwanta sannan wadansu mutane sama da 10 sun yi batan dabo a Vietnam, sakamakon kadawar mahaukaciyar guguwa da ake wa lakabi da Yagi, wace ta kada a tsakiyar ranar Asabar.

Kamfanin dillacin labarai na VNExpress ya ruwaito cewa mahaukaciyar guguwar ta Yagi mai zuwa tare da ruwan sama da iska mai karfin kilomita 230 a cikin sa'a guda ta kuma yi awon gaba da dubban bishiyoyi da kuma kwale-kwale a lokacin da ta kada a Asabar din nan a lardinan Quang Ninh da Haiphong da ke Arewacin Vietnam.

Bugo da kari masu aiko da rahotanni sun ce mahaukaciyar guguwar da ka iya zama mafi karfi da ba a taba gani irinta ba a cikin shekaru 10 da suka gabata, ta yi kaca-kaca da rufin gidaje da kuma allunan tallace-tallace da ke girke a tituna.

Dama dai kafin kadawarta a Vietnam, guguwar ta Yagi ta yi ajalin mutane biyu a Kudancin China tare kuma da jikkata wadansu mutanen 92 baya ga haddasa gagarumin ta'adi.