Maduro ya ce zai murkushe 'yan adawa
March 6, 2019Talla
Sai dai a daya hannun Maduro ya yi alkawarin murkushe wadanta ya kira " mahaukatan tsirarun kasar" da ke kokarin ganin cewar sun kifar da gwamnatinsa..
Shugaban majalisar wakilan kasar mai shekaru 35 da haihuwa, ya samu kyakkyawar tarba jiya da ya koma gida, bayan barin kasar a wata ziyarar kwanaki 10 da ya kaiwa mukarrabansa da ke yankin kudancin Amurka.
Guaido ya komo gida ba tare da an capkeshi kamar yadda gwamnati ta sha alwashin yi ba.