1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun gaza nasara a Guinea Bisau

Abdourahamane Hassane LMJ
February 2, 2022

Shugaban kasar Guinea Bisau Umaro Sissoco Embalo ya tsallake rijiya da baya, a wani yunkurin juyin mulkin da sojoji suka gaza samun nasara.

Guinea Bisau I Dakaile juyin mulki, mutane da dama sun halaka
Shugaba Umaro Sissoco Embalo na Guinea BisauHoto: Alui Embalo/AFPTV/AFP/Getty Images

An dai kwashe kusan sa'o'i biyar ana musayar wuta da manyan makaman atilare, tsakanin sojoji da ke yin biyayya ga gwamnati da kuma masu neman hambarar da shugaban kassar da kawo yanzu ake cikin kokarin tantance su. Barin wutar dai, ya rutsa da Shugaba Umaro Sissoco Embalo na Guinea Bisau din yayin da yake tsakiyar taro da majalisar ministocinsa a fadarsa. Jim kadan bayan dakarun gwamnati sun yin nasarar murkushe yunkurin juyin mulkin, Shugaba Embalo ya kira taron manema labarai inda ya bayyana cewa bai san wadanda suka kitsa juyin mulkin ba amma ya san wadanda ke adawa da matakan da ya dauka game da yaki da masu fataucin miyagun kwayoyi ba za su rasa hannu a ciki ba: "An mutu sossai, ban san adadin mutanen da suka mutu ba kawo yanzu. Daga kowane bangare an samu asarar rayuka, ina jinjinawa sojojinmu da suka dakile juyin mulkin."

An yi ta musayar wuta tsakanin sojoji, a yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara baHoto: Stringer/REUTERS

Shugaba Umaro Sissoco Embalo tsohon janar na soja da ke da shekaru 49 a duniya, ya dare karagar mulki tun a shekara ta 2020 bayan da ya samu nasara a zaben shugaban kasar da 'yan adawa ba su amince da sakamakon ba. Watanni da dama ke nan, suke takun saka da firaminstansa Nuno Gomess Nabiam wanda ya yi barazanar tsigewa tare da rusa majalisar dokoki. Kungiyar Tarayyar Afirka AU da Majalisar Dinkin Duniya, sun yi tir da juyin mulkin tare da nuna kin amincewa da matakin sojoji na kifar da mulki a wasu kasashen yankin yammacin Afirka, bayan abin da ya faru a Mali da Guinea Conakry da kuma Burkina Faso. Kasar ta Guinea Bisau mai yawan al'umma miliyan biyu wacce ke raba iyaka tsakaninta da Senegal da Guinea Conakry, ta saba fuskantar juyin mulki. Tun bayan da ta samu 'yancin kai daga Portugal a shekara 1974 juyin mulki hudu aka yi, na baya-baya nan shi ne a shekara ta 2012.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani