1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Babu takamaimen ranar zabe a Guinea Conakry

Mouhamadou Awal Balarabe
January 5, 2024

Sojojin da suka karbi mulki a ranar 5 ga Satumban 2021 sun kasa gabatar da takamaiman jadawalin zabe domin komawa ga tsarin mulkin dimukaradiyya

Guinea | Jagoran mulkin soji Mamadi Doumbouya
Hoto: Souleymane Camara/REUTERS

A jawabinsa na karshen shekara, shugaban gwamnatin mulkin soja Kanar Mamadi Doumbouya ya sanar da shirya zaben raba gardama a 2024ba tare da bayyana ranar da za a gudanar da zaben ba. Sai dai wannan mataki ya sanya shakku kan alkawarin sojoji na mika mulki ga farar hula...

Shekara guda kafin kawo karshen wa’adin mulki rikon kwarya da sojoji suka dibar wa kansu domin samun damar aiwatar da manufofinsu, ‘yan kasar Guinea Conakry da dama sun damu kan alkawuran da gwamnatin mulkin sojan ta dauka na mika mulki ga zababbiyar gwamnati.

Karin Bayani: Juyin mulki a Afrika gazawar dimukuradiyya

Hoto: Radio Television Guineenne/AP Photo/picture alliance

A bayyane yake cewa, kusan shekaru biyu bayan juyin mulkin, har yanzu kasar ta Guinea ba ta da rajistar masu kada kuri'a, kuma ba a gabatar da jadawalin zaben ba, walau na shugaban kasa ko na 'yan majalisar dokoki da na kananan hukumomi. Saboda haka Ibrahima Ballaya Diallo, daya daga cikin shugabannin kungiyoyin farar hula yake taka-tsan-tsan game da sanarwar gudanar da zaben raba gardama a 2024 da sojoji suka yi alkawari, yana mai zargin su da bullo da wata dabara don ci gaba da mulki.

"Wadannan kalamai ne kawai na fatar baki da ya ambata game da zaben raba gardama kan kundin tsarin mulki. Ina jira in gani a kasa. Mu a matsayinnu na jami'an da ke kula da zamantakewar jama'a a Guinea, mun yi saurin jan hankali game da hadarin da ke tattare da barin wannan gwamnatin rikon kwarya ta ci gaba ba tare da sanin alkiblar da ta dosa bisa manufa ba."

Hoto: BRENDAN MCDERMID/REUTERS

Baya ga sanarwar gudanar da kuri'ar raba gardama wanda ba a san ranar da zai kasance ba, batun da ya fi daukar hankali shi ne abubuwan da hukumomin Conakry suka gabatar a gidan talabijin na kasar, inda suka yi ikirarin cewar wani jami'in soja ya yi wa Mamadi Doumbouya yunkurin juyin mulki amma sun yi nasarar dakile shi, lamarin da ya ci gaba da haifar da shakku a Guinea Conakry da kuma a kasashen waje. Dalili kuwa shi ne, wannan zargin kulla makirci sun yi kama da makarkashiya da dan kama karya Sékou Touré ya rinka kullawa don kawar da abokan hamayyarsa. Ga abin da Mamadou Dian Baldé ke cewa a kan wannan batu

"Guinea, tun daga mulkinta na farko, ta kasance mai kulla manakisa a barikin Camp Boiro domin murkushe mutane da yawa kamar manyan 'yan boko da ke adawa da soja. Don haka wannan kasa ce da ba za ta iya rabuwa da tsofuwar ta'ada ta makirci ba."

Karin Bayani: Shekaru biyun mulkin soja a Guinea Conakry

Tuni ma dai Abdouramane Sano da ya kasance shugaban rikon kwarya na kungiyar Citoyen pour la République, ya ce hanyar da ake amfani da ita don tursasa mutane ga amsa laifi ta saba wa dokokin mutunta hakki da yancin 'yan kasa.

“Suna cewa an yafe musu, wai shin da an same su da laifi ne? shin hakan bai nuna irin rashin kimar kasar da za ta iya kama mutane ba, ta sanya su a gidan yari a tsawon lokacin da take so, sannan ta sake su kuma ta ce mu su su nemi gafara ?"

Hoto: Souleymane Camara/REUTERS

A fannin 'yancin fadin albarkacin baki ma dai, yanayin na ci gaba da tabarbarewa tsakanin gidajen rediyo da talabijin masu zaman kansu  da kuma gwamnatin mulkin soja a daya hannun. Ko da a baya-bayannan sai dai fadar mulki ta Conakry ta bukaci tashar Canal+ ta Faransa da ta daina watsa shirye-shirye masu nasaba da siyasa.

Kazalika, hukumomin sun takaita shiga yanar gizo da shafukan sada zumunta a kasar, lamarin da Ibrahima Ballaya Diallo na kungiyoyin farar hula ya yi tir da shi.

"Mun shafe fiye da kwanaki 40 ba tare da intanet ba, an rufe kafafen yada labarai. Sannan an tilasta wa kafafen yada labarai da ke son sake budewa yin alkawalin cewa, ba za su kara watsa shirye-shiryen da ke da nasaba da siyasa ba. Wane dan kasuwa ne zai ga irin wannan salon shugabanci kuma ya zuba jari a kasar nan?"

Sama da shekaru biyu ke nan da aka hana taruka da gangami da sauran zanga-zangar siyasa a kasar Guinea. Sannan an tilasta wa manyan shugabannin adawa gudun hijira a kasashen waje.