1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Guinea Conakry za ta yi zaben kasa a 2025

March 18, 2024

Sabon Firaminstan kasar Guinea ya ce ba za a gudanar da zabe cikin shekarar nan ba kamar yadda aka tsara tun da farko.

Hoto: John Wessels/AFP

Firaminstan ya ce akwai shirye-shirye da dama da ba a kammala ba don haka yanzu zabe sai karshen shekarar 2025. Sabon Firaiminstan na Guinea Conakry Amadou Oury Bah, ya ce kayyade  lokacin mika mulki ya ta'allaka ne da shirin da ake da shi a  kasa ciki har da yi wa harkar gudanar da mulki garambawul.

Karin bayani: Guinea Conakry: Shakku kan alkawarin zabe

Ya ce ga Guinea ma akwai tsare tsare da dama wadanda sai an bi su sau da kafa kafin a diga wa mulkin soji aya kuma wadannan shirye-shirye a cewarsa za su kai karshen shekara. To sai dai fa 'yan hamayya sun bayyana kalaman na Oury a matsayin masu sanya rashin yarda da aminci, kuma ba za su lamunci hakan ba.

Tuni 'yan kasar dai suka fara bayyana yadda suka ji da sanarwar ta jinkirta zabe da Firaminsta Oury ya yi.

"A matsayina na uwa ina bukatar ci gaba a kasata amma ba da mulkin soja ba, saboda idan sojoji ne ke mulki hakan ba mai yiwuwa bane. Don haka dole ne su nade ya nasu ya nasu su bar kujerar mulki kamar yadda suka yi alkawari a ranar 31 ga watan Disambar 2024."

Shi ma dai wannan matashin bai amince da ci gaba da mulkin na soji ba a kasarsa ta haihuwa

Kawai sun yi magana ne don su dadada wa sojoji. bamu bukatar haka, dole ne su sauka daga mulki a ranar 31 ga watan Disambar wannan shekarar ko suna so ko basu so". 

Karin bayani: Guinea ta sanar da gudanar da zaben raba gardama

Ousmane Diallo matashin dan Conakry ne kuma ya ce shi ma 31 ga watan Disamba kawai ya ke jira ya ga ficewar sojojin.

"Dole ne fa sojin nan su kara wuta wannan shekarar. dukkan abubuwa da tsohon shugaban kasa Alpha Conde ya bari kamar wutar lantarki sun lalata su, ga kuma farashin kayan masarufi da yayi tsananin tsada a kasuwanni, fatara na karuwa cikin kasa."

Dama dai daga cikin tsare-tsare da aka yi na mika mulki ga farar hula cikin shekarar nan shi ne yin zaben raba gardama domin gyara kundin tsarin mulki da yin kidaya wadda za ta samar da jadawalin bayananan mutanen da za su kada kuri'a kuma an shirya kammala komai da komai cikin watanni 36 tun bayan juyin mulki.

Ibrahim Diallo shugaban gudanarwa ne na kungiyar da ke hankoron kare kundin tsarin mulki kuma ya ce akwai wasu dabarbaru maimakon jinkirta zabe.

"Ya na kan tsari idan muka ce za mu yi magana kan sake fasalta kasa, kuma za mu iya neman hukumomin kasa da kasa su taimaka mana ta fannin kudi domin magance matsalar tattalin arziki da ke damun mu, amma ba a lokacin sauyin mulki za mu yi tunanin inganta kasarmu ba ko kuma kokarin sake fasalta tsarin gudanarwa gaba daya ba."

Sojoji dai sun karbe mulki a Guinea ne da bakin bindiga bayan sun hambarar da zababben shugaban kasar Alpha Conde tare da alkawarta wa kungiyar habaka tattalin arziki ta yammacin Afrika ECOWAS da kuma kasashen waje cewa za su mayar da Guinin karkashin turbar dimokradiyya a karshen 2024.

Karin bayani: 'Yan sandan Guinea sun yi arangama da masu bore

Dr Eduard Zoutoumou, dan adawa ne kuma ya ce kalaman na Firaminista Oury sun kawar da yarda da ke tsakanin sojin da talakawa, sannan ya zargi orin da komawa bangaren sojoji don haka ya ce ba za su lamunci wani karin lokaci ba idan wannan shekarar ta kare.

"Mr Bah Oury, shi ne mutumin da nake ganin mai kura da fatar akuya tunda yanzu yana so ya taimaka wa sojoji su maida 'yan adawa marasa bakin magana ko kuma su kauda su ma idan suka samu dama domin su ci gaba da mulki. Ina tunanin Mr Doumbouya, shugaban mulkin soji na kokari ne ya fito takara. abunda muka sani shi ne ranar 31 ga watan Disambar 2024 mulkin soja zai kare ba za mu lamunci duk wani abu bayan nan ba.".

'Yan hamayya da kuma sauran kungiyoyi dai sun zargi ECOWAS da karfafa wa sojojin gwiwa su yi ta mulkinsu a Guinea. Wannan sanarwar dai ta  kara lalata dangantakar da ke tsakanin sojin da kuma bangaren adawa wadanda tun dama ke zaman 'yan marina. To amma dai duk da haka, 'yan hamayyar sun bukaci magoya bayansu su kwamntar da hankali tare da jiran mataki na gaba da jagororinsu za su dauka.