1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guinea na son soke lasisin kamfanin hakar ma'adinai na Dubai

May 7, 2025

Mahukuntan kasar Guinea sun dauki hanyar soke lasisin hakar ma'adinan kamfanin EGA mallakin Hadaddiyar Daular Larabawa. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ne ya sanar da samun tabbacin hakan a wannan Laraba.

Hoto: uncredited/AP/picture alliance

Kamfanin EGA ya fara samun takun-saka da gwamnatin Guinea tun a watan Oktoba na bara, lokacin da sojojin da ke mulkin Guinean suka dakatar da wasu ayyukan kamfanin, bisa rashin bin ka'idar harajin kwastom na kasar.

Matakin kasar ta Guinea na nuna wani sabon yanayi inda kasashe masu arzikin ma'adanai a yankin Afirka ta Yamma ke neman samun cikakken iko da albarkatun kasarsu, matakin da ka iya sauya masana'atun hakar ma'adinai a duniya.

Kamfanin na Hadaddiyar Daular Larabawa da Guinea ta dakatar ya fara aiki a Guinea a shekarar 2019, kafin juyin mulkin da aka yi a kasar.

Gwamnatocin soji da ke jagorantar kasashen Guinea, Mali, Nijar da Burkina Faso sun dage kan kwaskwarima ga dokokin hakar ma'adinai da bayar da kwangiloli masu nasaba da hakan, tsare shugabannin kamfanonin hakar ma'adinai, dakatar da ayyuka, da kuma kwace kayayyaki yayin da suke bukatar bude wa kasashensu kofofin samun karin kudin shiga