1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kasar Guinea ta shirya dawo wa kan dimukradiyya

January 1, 2024

Shugaban gwamnatin mulkin sojin kasar Guinea, Colonel Mamady Doumbouya, ya sanar da gudanar da zaben raba gardama da zai sake mai da kasar kan turbar dimukradiyya a 2024.

Hoto: uncredited/AP/picture alliance

Shugaban gwamnatin sojin kasar Guinea Conakry, Colonel Mamady Doumbouya, ya sanar da gudanar da zaben raba gardama da zai sake mai da kasar kan turbar dimukradiyya a wannan shekara ta 2024.

Duk da cewa bai sanar da takamammen lokacin gudanar da zaben ba, shugaban ya ce yana da yakinin gudanar da zaben da zai bai wa kowanne 'dan kasar 'yanci da kuma burin ciyar da kasar gaba, kamar yadda ya shaida a jawabin da ya yi wa 'yan kasar ta sabuwar shekara, 2024.

Tun bayan hambarar da gwamnatin Alpha Conde, a shekara ta 2021, kasashen duniya sun yi ta matsin-lamba ga Colonel Doumbouya, na dawo da mulkin kasar kan tafarkin dimukradiyya, wanda daga bi sani ya yi alkawarin mika mulki ga farar hula a shekara ta 2026.

Juyin mulkin Guinea Conakry, na daga cikin mafarin da suka sanya 'damba ga wasu kasashen yammacin Afrika na hambarar da gwamnatin dimukradiyya irin su Mali da Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso.