Guinea za ta bada gudummowar Sojoji zuwa Somaliya
July 23, 2010Talla
Ƙungiyar Tarayyar Afrika ta sanar da kara yawan dakarunta na kiyaye zaman lafiya a Somaliya da gudummowan sojoji daga ƙasar Guinea. Wannan sanarwar tazo ne ayayin, taron ministocin ƙungiyar gabannin buɗe taron shugabanninta na 15 a gobe, taron dake zuwa kasa da makwanni biyu bayan da ƙungiyar al-Shabaab ta Somaliya ta kai hari a Kampala.
shugaban AU Jean ping ya faɗawa taron manema labaru a birnin Kampala cewar, Guinea ta shirya tura dakarun nata, akan kimanin dubu 8 da yanzu ke girke a Somaliyan dake fama da rigingimu. Ya kara da cewar, suna fatan cikanta dakarun kiyaye zaman lafiyan na haɗin gwiwar zuwa dubu 10.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Edita: Umaru Aliyu