Gurɓacewar muhalli a kudancin Najeriya
March 19, 2015Talla
Ƙungiyar ta Amnesty ta yi kashedi dangane da bazarnar ƙara samun gurɓacewar muhali a kudancin Najeriyar a sanadiyyar malallar ɗanyan man fetur.Hakan kuwa ya biyo bayan wani rahoton da ƙungiyar ta bayyana wanda a cikinsa ta ce a shekara bara da ta shige ta 2014.
Kamfanon aiki haƙon man fetur ɗin na Shell na Ingila da Eni na Italiya waɗanda ke gudanar da aiyyukansu a Najeriyar sun ce sun haddasa gurɓacewar muhali a wurare 553.Ƙungiyar ta ce wannan addadi da kamfanonin suka bayyana na ɗaga hankali sossai, kuma ta ce ya zama wajibi a farka daga barci tun da sauran wuri.