1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Karuwar gurbacewar iska a duniya na kashe rayuka

Abdourahamane Hassane
June 19, 2024

Gurbacewar iska ta cikin gida da waje na kashe mutane da dama a duniya ciki har da yara, kuma yanzu ta fi shan taba sigari illa a cewar wani rahoto da asusun yrara na MDD UNICEF ya bayyana.

Hoto: Miho Kibiki/The Yomiuri Shimbun/AP Photo/picture alliance

  Fiye da mutane miliyan takwas, ciki har da yara dubu 700,000 'yan kasa da shekaru biyar, suka mutu a shekarara ta  2021 saboda gurbataccen iska. Sanadin mace-macen yaran yana da nasaba da dafa girki da gawayi, wanda mafi yawancinsu suka mutu a Asiya daAfirka.