1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gurbacewar ma'amala tsakanin Faransa da Turkiyya

January 24, 2012

An shiga takon sako tsakanin Faransa da Turkiyya game da batun kisan armeniyawa.

Members of Turkish associations in France demonstrate to protest against a French Parliament's bill outlawing Armenian genocide denial, in front of the Assemblee Nationale in Paris, France on December 22, 2011. France's Parliament is set to debate a bill that would make it illegal to deny that Turkey’s massacre of ethnic Armenians in 1915 was an act of genocide. Photo by Alain Apaydin/ABACAPRESS.COM # 302396_007
Hoto: picture-alliance/dpa

Kudurin dokar da Majalisar dattawan Faransa ta gabatar, wanda ya tanadi hukunta duk wanda ya karyata zargin aikata kisar gilla kan Arminiyawa ya sha kakkausar suka daga Frime Ministan Turkiya, Recep Tayyip Erdogan inda ya ce kudirin dokar ya nuna banbanci da kuma wariyar launin fata. Frime Ministan wanda ya bayyana hakan lokacin wata ganawar da yayi da 'yan majalisar wakilan kasar, ya ce wannan matakin ya take 'yancin walwala wajen tunani. Ya kuma jaddada cewa wannan kudurin doka ko daya ba zai yi taseeree a kasarsa ba sa'anan ya kara da cewa gwamnatinsa zata dauki wadansu matakai wadanda bata fayyace ba idan har wannan kuduri ya zama doka.

A ranar litinin da ta gabata, Majalisar dattawan Faransa ta amince da wani mataki wanda ya tanadi hukuncin dauri a gidan yari a Faransa wa duk wanda ya karyata cewa kisan kiyashin da dakarun Turkiyya, a zamanin mulkin Daular Ottomaniya, suka yi wa Arminiyawa ba babban laifin yaki bane. Bisa dukkan alamu dai Faransa bata da niyyar canza ra'ayinta dangane da wannan mataki, to sai dai Erdogan ya ce ya bada gaskiyar cewa Faransa zata gyara kuskuren da ta yi nan ba da dadewa ba.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba

Ediota: Yahouza Sadissou Madobi