1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus: Shari'ar masu ra'ayin NAZI a Dresden

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 23, 2026

Matasa takwas da ake zargi da zama mambobin wata kungiya ta masu tsattsauran ra'ayi da ke yunkurin samar da gwamnati mai ra'ayin 'yan Nazi, sun gurfana a gaban kuliya a birnin Dresden da ke gabashin Jamus.

Jamus | Matasa | Kotu | Dresden | Ra'ayi | Nazi | Adolf Hitler
Guda daga cikin matasan da aka gurfanar a gaban kuliya bisa zargin ra'ayin 'yan NAZIHoto: Sebastian Kahnert/dpa/picture alliance

Masu shigar da kara sun yi amannar cewa, mutanen mambobin kungiyar 'yan awaren Saxon ne da aka kafa a shekara ta 2020 da mambobi kimanin 20. Kungiyar, na yada manufofin kyamar baki da kyamar Yahudawa da kuma tsattsauran ra'ayin addinin Kirista. Masu shigar da karar sun bayyana cewa, kungiyar ta 'yan awaren Saxon ko kuma SS a takaice ta yi amannar Jamus za ta rushe nan da wani lokaci, kuma za su yi amfani da wannan dama su kafa kasa mai akidar jagoran 'yan Nazi Adolf Hitler.

 

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW