Gurfanar tsohon mai binciken kudin Masar a kotu
April 12, 2018Talla
Lauyan rundunar sojojin kasar ta Masar Ali Taha ya bayyana wa manema labarai cewa za a fara shari'ar tsohon babban mai binciken kudin a ranar 16 ga wannan wata na Afrilu da muke ciki. Shi dai Genena an kama shi ne tun a watan Fabrairun wannan shekara, yayin da ya sanar da cewar tsohon shugaban gudanarwar rundunar sojojin Masar Sami Annan ya mallaki wasu takardun sirri masu alaka da shugabancin kasar.
Sojojin kasar dai sun chafke shi jim kadan bayan ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a yayin zaben da aka gudanar a watan Maris din da ya gabata, dai-dai lokacin da masu adawa da shugaban kasar Abdel-Fattah el-Sissi ke fuskantar dauki dai-dai saboda bayyana aniyarsu ta ja da Sisi a takarar shugabancin kasar.