Guterres na ziyarar gaggawa a Somaliya
March 7, 2017Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya kai wata ziyarar gaggawa a wannan ranar Talata zuwa Somaliya don sake duba na keke da keke kan bala'in fari da ya addabi al'ummar wannan kasa, inda ya gana da sabon shugaban kasar da ya bayyana cewa kasar na cikin babban bala'i na 'yunwa da ke bukatar a kai mata agaji na gaggawa.
Sakataren na Majalisar Dinkin Duniya da saukarsa a wannan kasa da ke a yankin kahon Afirka ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa mutane na mutuwa, ya kuma zama dole akai musu daukin gaggawa. Guterres ya ce kiran ya zama dole duba da yadda abubuwan suka cude ga rikici da fari da sauyin yanayi ga cututtuka da kwalara hada wadannan abubuwa lokaci guda ba karamin tashin hankali ba ne.
Kasar ta Somaliya dai na zama daya cikin kasashen da aka yi shelar neman musu agaji na Dala miliyan dubu hudu a watan da ya gabata, sauran kuwa su ne Najeriya da Yemen da Sudan ta Kudu da suke fuskantar irin wannan matsala a wasu yankunansu.