Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya na ziyara a Iraki, a daidai lokacin da al'ummar kasar ke zanga-zangar adawa da sauya kundin tsarin mulki.
Talla
Ziyarar sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniyar António Guterres na zaman ta farko cikin shekaru shida, tun bayan shelanta kawo kungiyar 'yan ta'addan IS. Ziyarar tasa kuma na zuwa ne a daidai lokacin da ake cika shekaru 20 da kawar da mulkin Shugaban Saddam Hussein da sojojin Amurka suka tunbuke shi bayan da kaddamar da yaki a kasar. Yayin ziyarar ta Guterres dai, bayan ganawa da mahukuntan Irakin da kungiyoyin kare hakkin dan Adam da na masu rajin kafa dimukuradiyya, ya ce ya ziyarci kasar ne domin karfafa guiwa ga al'ummarta da ke murmurewa daga ta'annutin kungiyar IS shekaru biyar din da suka gabata. Bayan nuna goyan baya ga al'ummar ta Iraki da jinjina musu da ya yi kan nasarar tunkarar tarin kalubalen tsaro da na zamantakewa da yunkurin tarwatsa kasar da suka yi, Guterres ya jaddadawa shugabanin na Iraki muhimmancin hadin kai da hakurin zama da juna domin sake gina kasar da samun ci-gaba.
Iraki na cikin tashin hankali
Matsalar rashin aikin yi da ta cin hanci: Tsawon kwanaki dubban al'ummar Iraki ke zanga-zanga. Dokar hana zirga-zirga ba ta hana su yin zanga-zangar ba. Gwamman mutane sun rasa ransu, sama da 1600 kuma sun jikkata.
Hoto: Getty Images/AFP/A. Al-Rubaye
Ranakun tashin hankali
Duk da alkawarin kawo gyara daga gwamnati, zanga-zangar nuna adawa da cin hanci da matsin tattalin arziki, na ci gaba a Iraki. Ko da a ranar Jumma'a, mutane sun taru a wasu wurare da ke tsakiyar Bagadaza babban birnin Irakin, haka ma a kudancin kasar.
Hoto: Reuters/W. al-Okili
Ba a daina zanga-zangar ba
Ya kamata dokar hana zirga-zirga da aka sanya bayan kwashe kwanaki ana bata kashi ta sanya al'amura komawa daidai. Ofishin hukumar kare hakkin dan Adam a Bagadaza ya ce kimanin mutane 38 ne suka halaka, 35 daga cikinsu masu zanga-zangar ne yayin da wasu 1600 suka jikkata. Masu zanga-zangar da dama sun bijirewa dokar hana zirga-zirgar, inda suke kwana a kan tituna.
Hoto: picture-alliance/AP Photo/H. Mizban
Zanga-zanga ba tare da jam'iyya ba
Zanga-zangar ta sha bamban da ta halin kuncin rayuwa da aka saba yi a Iraki. A wasu yankunan ana samun hasken wutar lantarki na tsawon sa'o'i hudu kacal a rana. Babban bankin duniya ya ce kaso 25 na matasan kasar ba su da ayyukan yi. Babban malamin Musulmi mabiya mazhabar Shi'a a Irakin Ali al-Sistani ya yi kira da a gudanar da gagarumar kwaskwarima a harkokin gudanarwa kafin lokaci ya kure.
Hoto: Getty Images/AFP/A. Al-Rubaye
An rufe ko ina
Da fari an shirya yin zanga-zangar ba tare da tuta ko katuna dauke da rubutu ko kuma taken wata jam'iyya ba. Sai dai abubuwa sun rincabe bayan korar wani fitaccen janar na soja Abdel-Wahab al-Saadi. A Bagadaza, masu zanga-zangar sun yi kokarin shiga wani yanki da ake kira da "Green Zone." A wannan yanki da ke cike da tsaro, akwai ofisoshin gwamnati masu yawa da ofisoshin jakadancin kasashen waje.
Hoto: Getty Images/AFP/A. Al-Rubaye
Zargin 'yan sanda da cin zarafi
Jami'an tsaro na amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar. Ofishin kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya a Geneva, ya zargi 'yan sanda da amfani da harsasai na gaske da na roba. An soki firaminista Adel Abdel Mahdi bisa yabawa jami'an tsaron da ke amfani da karfi wajen murkushe zanga-zangar da kuma dora alhakin cin zarafin kan wasu mutane da bai bayyana ba da ya yi.
Hoto: picture-alliance/AP Photo/K. Mohammed
Kira domin yin taka tsan-tsan
Shugaban kasar Iraki, Barham Saleh (Hoto, Maris 2019), ya yi tir da tashe-tashen hankulan tare da bukatar yin taka tsan-tsan da kuma bin doka. Saleh ya nunar da cewa kundin tsarin mulkin kasar ya bayar da damar yin zanga-zangar lumana. Kwamitin kare hakkin dan Adam na majalisar dokokin Irakin, ya yi tir da matakin murkushe masu zanga-zangar da karfin tuwo.
Hoto: picture-alliance/AP Photo/F. Belaid
Hotuna 61 | 6
Ya kuma yi kira ga 'yan siyasa da su mutunta yarjejeniyar fahimtar juna da suka cimma tsakaninsu, domin ganin an gudanar da zaben da zai samar da kwanciyar hankali da ci-gaban kasa. Ba ya ga haka kuma, ya yi bukaci da a samar da wani tsarin afuwa na gama-gari da zai bai wa dubban Irakawan da ke samun mafakar siyasa a ketare damar komawa kasarsu su kuma gina ta. A nasa bangaren firaministan kasar Mohammed Shia al-Sudani wanda ya yi godiya ga sakataren na Majalisar ta Dinkin Duniya a madadin al'ummar Iraki kan irin goyan bayan da yake ba su, ya kara da bayyana masa irin kokarin da gwamnatinsa ke yi na ganin an tabbatar da zaman lafiya da tsaro ba a kasar ta Iraki kadai ba harma da yankin baki daya. Kasar Iraki da ke da dimbin arzikin man fetur baya ga kudin ajiya a asusunta da ya kai dala biliyan 100 dai, na fama da matsalolin tsaro da cin-hanci da rashawa sakamakon kabilanci da bangaranci gami da tsoma bakin kasashen ketaren. Wannan lamari dai ya sanya matasan kasar da ke kishirwar samun sauyi, gudanar da tarin zanga-zangar da ake fatan 'yan siyasar kasar za su shawo kanta ta hanyar yi wa tufkar hanci.