Rashin yarda na barazana ga hadin kan duniya
September 25, 2018Talla
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a wannan Talatar ya bude taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya tare da kashedi da babbar murya game da karuwar rudani da rashin yarda a tsakanin kasashe wanda yace yana barazana ga hadin kan duniya.
Da yake jawabi ga zauren Majalisar Antonio Guterres yace rashin aminci a tsakanin kasashe ya sa lamura cikin mawuyacin hali.
Sai dai kuma bai ambaci wani ko kuma zargin wani bangare ba.
Guterres ya kuma yi amfani da wannan dama inda ya kara yin kira game da barazanar da duniya ke fuskanta game da sauyin yanayi. Yana mai cewa sauyin yanayi na faruwa cikin gaggawa fiye da yadda ake tsammani.