Guterres: UNRWA na nan daram, babu sauyi
October 29, 2024Talla
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce dokar Isra'ila ta haramta aikin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNRWA zai iya haifar da mummunan sakamako ga Falasdinawa 'yan gudun hijira a yankunan da Isra'ila ta mamaye. Yana mai cewa ko kadan ba a lamunci hakan ba.
Guterres ya ce yayin da ake cikin wannan tsanani, aikin UNRWA ya fi zama wajibi a yanzu fiye da kowane lokaci a baya kuma ba za a iya maye gurbinta ba. Ya ce aiwatar da wadannan dokoki da Isra'ila ta yi zai kasance koma baya ga yunkurin warware rikicin Isra'ila da Falasdinawa don dorewar zaman lafiya da tsaro a yankin baki daya. Guterres ya ce zai gabatar da batun ga babban zauren Majalisar Dinkin Duniya mai wakilan kasashe 193