1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Guterres ya bayyana damuwa kan kisan mutane a Gaza

November 1, 2023

Yayin da aka shiga kwana na 26 da barkewar rikici a zirin Gaza, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antoniyo Guterres ya bayyana damuwa kan ruwan bama-bamai da dakarun Isra'ila ke yi wa dan karamin yankin na Falasdinu.

Guterres ya bayyana damuwa kan kisan mutane a GazaHoto: Xie E/Xinhua/picture alliance

A cewar mai magana yawusa, Guterres ya ji takaicin abin da ke faruwa a zirin Gaza musanman kisan da ake yi wa Falasdinawa da suka hadar da mata da yara kanana sakamakon luguden wutar da Isra'ila ke yi wa zirin ciki har da sansanin 'yan gudun hijira Jabaliya mai tarin jama'a.

Karin bayani: Isra'ila ta ce sojojinta sun kai hare hare dubu goma sha daya kan Hamas

A daya gefe kuma Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya yi kakkausar suka a game da karuwar hare-haren ba kakkautawa da Isra'ila ke kai wa zirin na Gaza, wadanda kawo yanzu suka yi ajalin yara fiye da 3,500.

Karin bayani: Yakin Gaza ya hallaka mata da kanana yara kusan dubu shida

Asusun ya kuma bayyana damuna kan mokomar yaran da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su tun a ranar bakoye ga watan Oktoba da ya shude a daidai lokacin barkewar rikicin.