Antonio Guterres ya ce akwai matsala a yakin Isra'ila a Gaza
November 9, 2023Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce adadin rayuka da ke salwanta a Zirin Gaza na tabbatar da cewar akwai matsalar a yakin da Isra'ila ta kaddamar a yankin a kan kungiyar Hamas.
Cikin wata hirar da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Reuters, Mr Guterres ya kuma ce kananan yaran da suka mutu a wannan rikici ya wuce kima.
A cewar jagoran na Majalsair Dinkin Duniya, hali na neman jinkai da ake gani a Zirin sakamakon halin da ake cikin na sanyaya gwiwar mutane a duniya dangane da yakin na Isra'ila a can.
Ma'aikatar lafiya ta yankin falasdinu dai ta ce sama da mutum dubu 10,500 ne suka mutu tun bayan tashin rikicin a ranar bakwai ga watan jiya.
A gefe guda kuma Antonio Guterres ya yi tir da garkuwar da kungiyar Hamas ta yi, da nufin hana afka mata.
Jakadan Isra'ila a Majalisar Dinkin Duniya Gilad Erdan, ya yi watsi da kalaman Mr. Guterres a game da yakin, yana mai cewa alkaluman da Hamas ke fitarwa na wadanda suka mutun, ba abu ne da za a yarda da su ba.