Guterres ya nemi a daina yaki a Ukraine
April 29, 2022Akalla mutane uku aka bada rahoton sun mutu a harin da Rasha ta kai a wani yanki na yammacin Kyiv babban birnin Ukraine. Wannan shi ne karon farko da ta kai hari babban birnin cikin makonni biyun da suka gabata, wanda ya zo a daidai lokacin da sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ke ziyara a Bucha da sauran yankunan da ake zargin Rasha ta aikata laifukan yaki.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar ya yi tsokaci kan abin da ya gani a wuraren da Rasha ta kai hare hare yana mai cewa: "Idan na ga irin wadannan gidaje da suka lalace, na kan yi tunanin cewa idan iyalina ne a wadannan gidaje da aka ragargaza kuma aka kona ya ya mutum zai ji. Na kan tunato cewa jikokina suna gudu cikin firgici, wasu daga cikin iyalai an kashe su."
A taron manema labarai na hadi gwiwa da suka gudanar, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce harin da Rasha ta kai a lokacin da sakataren Majalisar Dinkin Duniyar yake ziyara ba komai ba ne illa domin ta tozarta Majalisar Dinkin Duniyar da ma duk abin da ta ke yi. Ya ce abu ne mai muhimmanci da sakataren Majalisar Dinkin Duniyar ya ziyarci yankin Borodyanka na lardin Kyiv domin gane wa idanunsa ta'asar da Rasha ta aikata a can. Daruruwan al'umomi da biranen Ukraine sun fuskanci irin wannan abun da ya faru a Borodyanka da Bucha.
Ya ce: "Muhimmin batu a tattaunawar da muka yi da sakataren Majalisar Dinkin Duniya shi ne ta ya ya za a dakatar da wannan zalunci da Rasha ke yi. Kuma wannan ba wai batu ne a kan Ukraine ba kadai, batu ne da ya shafi makomarmu. Batu na makomar ita kanta Majalisar Dinkin Duniya da makomar dokokin duniya da kuma makomar kasashe da dama, ba kawai makwabtan Rasha ba wadanda mai yiwuwa a nan gaba su fada tarkon wannan mummunar aniyar ta Moscow ba."
Jamus ta yi Allah wadai da harin Rasha
Gwamnatin Jamus ta yi martani da kakkausar harshe kan wannan harin na Rasha da ta bayyana shi da rashin imani na makami mai linzami da ya fada birnin Kyiv. Mai magana da yawun gwamnatin ta Jamus Wolfgang Buechner ya ce shugaban Rasha Vladimir Putin ya nuna baya daraja kowa.
Ya ce: "Mun yi Allah wadai da harin makami mai linzami a Kyiv yayin ziyarar sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres wanda ya je domin tattauna hanyoyin samun masalaha."
A waje guda dai Antonio Guterres ya sake nanata kiran kawo karshen yakin. Antonio Guterres ya ce a ganawar da ya yi da Putin ya yi masa alkawarin bada damar kwashe fararen hula da suka makale a Mariupol "a bisa manufa na shigar Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar agaji ta Red Cross."
Tuni dai sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bar Kyiv bayan kammala ziyararsa a ranar Jumma'a