Guterres: Ba za mu shiga rikicin Venezuela ba
February 5, 2019Talla
Kasashen Mexico da Yurugai na shirin hada kan kasashen duniya tare da Majalisar Dininkin Duniya zuwa babban taro a Montevideo babban birnin kasar Yurugai a ranar Alhamis domin samar da mafita kan rikicin siyasar da ya barke a Venezuela. Rikicin shugabanci a Venezuelan dai ya raba kan kasashen duniya, inda kasahsen Amirka, Faransa da Jamus da Spain da Kanada da kuma Ostireliya ke nuna goyon bayansu ga jagoran adawa Juan Guido, yayin da Rasha da China ke tsayin daka ga Shugaba Nicolas Maduro.