1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafutukar yaki da cin zarafin mata a duniya

November 25, 2021

A Jamus, a Kowane kwana biyu da rabi, mace guda na rasa ranta sakamakon cin zarafi daga tsohon mijinta ko tsohon abokin zamanta. Wannan yana nufin cewa rikicin tsakanin ma'aurata ko masoya na karuwa.

Symbolbild Gewalt gegen Frauen
Hoto: imago images/Sven Simon

Bisa ga kididdigar da ta fito daga ofishin ‘yan sandan da ke kula da manyan laifuka a Jamus, mata 119,164 ne suka fuskanci cin zarafi daga abokan zama a bara. Wannan adadin ya karu da kusan kashi biyar bisa dari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, wanda ya hada da cin zarafin da zage-zage da tauye 'yancin walwala da kuma uwa uba kisa. Alkaluma sun nunar da cewa a kowace rana tsohon magidanci na yunkurin kashe abokiyar zamansa, inda a cikin shekara ta 2020, matan da suka rasa rayukansu ta wannan hanya suka karu .Yayin gabatar da rahoto game da cin zarafin mata a Berlin, ministar iyali ta Jamus Christine Lambrecht (SPD)  ta koka dangane da rufa-rufa da ake yi a kan yawan matan da ke shiga mawuyacin hali.

Rufa-rufa a kan yawan matan da ke shiga mawuyacin hali.

Hoto: Kevin Tschierse/DW

"A lokacin da na ji abin takaici da ya faru cewa wani tsohon magidanci ya kashe mata da ya rabu da ita da ‘ya'yansu, sai na ji tsikar jikina na tashi. Yanzu ba abin da ya shafi iyali ne kawai ba, amma abin takaici ne a ce tsohon abokin zama ya kashe mace da yara, ko ya zalince su. To wannan ba komai ba ne illa cin zarafi." Mata da yawa na tsoron tinkarar ‘yan sanda saboda suna ganin cewar ba za a yarda da bahasin da za su bayar ba. Ko da nazarin da aka yi a kan wannan batu sai da ya nuna cewa kashi 90 bisa 100 na matan na neman a sakaye sunansu idan suka shigar da kara. Amma hukumar 'yan sanda ta Jamus ta ce ba a samu karuwar cin zarafin mata a yayin dokar kulle corona ba, mai yiwuwa saboda ma'auratan ba su samu sukunin shigar da kara ba.Lina Stotz daga kungiyar kare hakkin mata ta Terre des Femmes Deutschland" ta ce cin zarafin matan ya  tsananta a Jamus. "Za a iya cewa abin da ke haddasa rikicin tsakanin ma'aurata ko abokan zama shi ne neman karfin fada a ji. Ma'ana abokin zama, galibin namiji na kokarin juya mai dakinsa ko abokiyar zamansa yadda yake so, kuma ya rabu da ita lokacin da yake so. Misali a nan shi ne: yawancin ma'aurata da suka rabu ko kuma lokacin da rabuwa ya kusa na canja hakinta. Wannan hali na fusata magidanci, kuma a wani lokaci ya na dukar mai dakinshi, lamarin da ke haifar da mummunan sakamako, saboda yana jin haushin rasa matar da yake ganin kamar mallakinsa ce. "

Hukunci a Jamus a kan masu cin zarafin mata

Hoto: imago images/photothek

A watan Fabrairun 2018 ne Jamus ta fara aiwatar da matakan da majalisar Turai ta dauka na yaki da cin zarafin mata. Wannan dai ya biyo bayan amincewa da kasashen duniya suka yi da yarjejeniyar Istanbul wacce ta tsara daidaiton jinsi kuma ta tanadi inganta halin rayuwar mata ta hanyar kare su tare da ilimantar da su. Saboda haka ne bayan amincewa da wannan kudiri, gwamnatin tarayyar Jamus ta samar da wani layin tarho na musamman da mata ke amfani da shi wajen yin korafi a kowane lokaci kuma ciki harsuna da dama. Sannan ana fatan samun wasu matakai daga gwamnati kawance ta SPD da Greens da kuma FDP da za a kafa nan gaba don kare hakkin mata, tare da samar da sabbin wuraren da za a tsugunar da su idan suka rabu da mazajensu ko masoyansu.

Ba a samu raguwar cin zarafin matan ba 

Hoto: imago images/Bernd Günther

Sai dai duk da gagarumin ci gaban da aka samu a cikin shekaru 20 da suka wuce, ba a samu damar rage cin zarafin mata yadda ya dace ba, in ji wata masaniyar zamantakewar al'umma Monika Schröttle daga cibiyar nazarin ilimin zaman lafiya (IfeS) da ke Nuremberg.Monika Schröttle: "Dalilin da ya sa har yanzu ake fama da cin zarafin mata shi ne, wani muhimmin bangare na dabi'ar dangantaka tsakanin jinsi bai canza kamar yadda ya kamata ba. Don haka har yanzu ba mu rabu da maza da ke nufa karfi da cin zarafin mata ba. Har yanzu ba a yarda da daidaito 'yanci da yanayin zamantakewa ba, musamman a tsakanin maza, don haka har yanzu wasu ke cewa: Ni na fi mace, ni ba mace ba ce." Wata cibiya ta Turai da ke sa ido kan mace-macen mata ta bayyana Spain a matsayin kasa daya tilo a Turai da aka samu raguwar mace-macen mata, saboda dokoki da aka dauka a kasar.