Koriya ta Arewa ta yi gwajin makami.
August 24, 2019Talla
Wannan dai shine karo na bakwai da Koriya ta Arewan ke harba irin wadannan makamai daga Arewa maso Gabashin yankin Hamgyong, tun bayan ganawar shugaban kasar Kim Jong Un da takwaransa na Amirka Donald Trump kan iyakokin yankin na Koriya a watan yunin bana. Mahukunta a Koriya ta Kudu sun bayyana takaici game da wannan barazana da makamai da suka ce suna fuskanta duk kuwa da cewar atisayen sojin hadin gwiwar tsakanin kasar da Amirka ya kammala tun farkon wannan mako, wanda dama shi ne ya kara haifar da tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Wannan hari na zuwa ne bayan da shugaba Trump na Amirka, ya shaidawa manema labarai a fadar mulki ta White House cewar akwai kyakkyawar fahimta a tsakaninsa da shugaba Kim na Koriya ta Arawan.