1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Gwamman mutane sun mutu a gidajen yarin Kwango

April 4, 2024

Sama da mutane 100 suka mutu a watanni hudun farko na 2024 sakamakon cunkoson gidajen yarin Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango, acewar wani jami'in hukumar kare hakkin 'dan adam na Majalisar Dinkin Duniya.

hotunan wasu masu zaman gidan yari
hotunan wasu masu zaman gidan yariHoto: Alfredo Zuninga/AFP

Mutanen sun mutu sakamakon kamuwa da cututtuka masu saurin yaduwa da kuma rashin tsafta a gidajen yarin da suka hadar da cutar tarin fuka da kuma karancin abinci harma da karancin kayan kula da kiwon lafiya, acewar jami'in hukumar kare hakkin 'dan adam.

Karin bayani:Fursunoni 900 sun tsere a Kwango 

Babban jami'in hukumar a Kwango Patrice Vahard, ya ce galibin mutanen sun rasa rayukansu a gidajen yarin da ke gabashin lardin Kivu da Tangayinka, sai kuma yankin Kwilu da ke arewaci.

Karin bayani: Kotu ta daure Vital Kamerhe a Kwango

Gidajen yarin Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango na daga cikin gidajen yari mafi cunkoso a duniya, acewar jami'an inda ya bada misali da dakunan masu zaman gidan wakafi da ya kamata a ajiye mutane 50 kacal, kimanin mutane 200 ke rayuwa a ciki a Kwango.