1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Al-Bashir zai fuskanci shari'a kan juyin mulkin 1989

Mohammad Nasiru Awal AH
July 20, 2020

Al-Bashir, wanda yake gidan wakafi saboda cin hanci, ka iya fuskantar hukuncin kisa idan aka same shi da aikata laifin juyin mulkin shekarar 1989.

Sudan Khartum | Prozess & Urteil Omar al-Baschir, ehemaliger Präsident
Hoto: picture-alliance/Anadolu Agency/M. Hajaj

Tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Sudan, Omar al-Bashir da aka kifar da gwamnatinsa bayan wani boren juyin juya hali a bara, a ranar Talata zai fuskanci shari'a game da juyin mulkin sojin da ya dora shi kan karagar mulki fiye da shekaru 30 da suka gabata.

Al-Bashir mai shekaru 76 a duniya, wanda yanzu haka yake gidan wakafi saboda cin hanci da rashawa, ka iya fuskantar hukuncin kisa idan aka same shi da aikata laifin juyin mulkin shekarar 1989, lokacin da ya hambarar da zababbiyar gwamnatin dimukuradiyya ta Firaminista Sadel al-Mahdi.

Shari'ar da ake masa tare da wasu mukarrabansa 16 na zuwa ne daidai lokacin da gwamnatin rikon kwarya ta Sudan ta kaddamar da jerin sauye-sauye a kasar.

Gwamnati a birnin Khartoum ta kuma yi alkawarin mika al-Bashir ga kotun kasa da kasa da ke hukunta manyan laifuka da ke zargin al-Bashir din da kisan kare dangi a rikicin lardin Darfur da ya hallaka mutum dubu 300 sannan miliyoyi suka rasa muhallansu.