Gwamnan Borno ya haramta sayar da fetur a Bama
May 10, 2025
Talla
Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito ofishin gwamnan jihar Babagana Umara Zulum na cewa wannan umurni na nan take da gwamnan ya bayar, yana mai cewa baya ga cikin garin Bama, matakin zai shafi sauran sassan karamar hukumar Bama.
Hukumomi a Maiduguri sun ce daukar wannan mataki ya zama wajibi domin rage samun man fetur ga 'yan ta'addar da suka sanyo jihar a gaba a baya-bayan nan.
Garin Bama da aka haramta sayar da fetur din shi ne mafi girma bayan babban birnin jihar Maiduguri, kuma yana kusa da dajin Sambisa, wata babbar maboya ta kungiyar 'yan ta'addan ISWAP.