Najeriya: Sulhu da mahara a Katsina
September 5, 2019Kananan hukumomi takwas ne dai a jihar ta Katsina da ke yankin Arewa maso Yammacin kasar, ke fama da hare-haren 'yan bindigar, da ya haddasa asarar rayuka da dukiyoyin al'umma masu tarin yawa. Gwamna Aminu Bello Masari dai ya sha alwashi karade daukacin kananan hukumomin da ke fama da hare-haren, inda kawo yanzu ya gana da 'yan bindigar daga kananan hukumomi hudu dasuka hadar da Sabuwa da Dandume da Faskari da kuma Kankara, tare kuma da jaddada tsananin bukatar zaman lafiya ga maharan.
"Abunda ya kawo mu nan shi ne muyi sulhu mu yafewa juna mu komo zamantakewar mu yadda take a baya. A da muna zuwa daurin auren juna da zanen suna, muna cin kasuwa guda mu kuma je jana'izar juna. Yau an wayi gari wadanda suke irin wannan huldar a tsakaninsu, sun koma suna kashe kansu. Mun zo ne domin muji korafe-korafen da ke damun mutane makiyaya me yake damunsu suma mazauna gari menene ke damunsu muma kuji abin da ke damun mu."
Shugabannin Fulani sun ce za su yi iyakar kokarinsu na ganin zaman lafiya ya dawo a jihar Katsinan, domin tuni suka zauna da 'yayansu da ke aika-aikar kuma sun amince za su bari. Mafi yawancin bukatun da Fulanin ke nunawa ga gwamnati dai sun hadar da samar musu da Ruga da asibitoci da makarantu da hanyoyi, inda da gwamnatin ta yi na'am da hakan.