1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanciNajeriya

Gwamnan Zamfara ya nuna yatsa ga Abuja kan tsaro

September 26, 2023

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare ya zargi gwamnatin tarayyar Najeriya da tura wata tawaga don yin sulhu da 'yan bindiga ba tare da saninsa ba, lamarin da fadar mulki ta Abuja ta musanta.

Gwamnan jihar Zamfara  Dauda Lawal Dare
Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal DareHoto: Dauda Lawal/Facebook

Gwamnatin jihar  Zamfara ta yi matukar kaduwa da samun wannan labari, ganin cewar kudin tsarin mulkin Nigeria ya tanadi cewa gwamna ne shugaban tsaro a jiharsa, amma gwamnatin tarayya ta yi kutse ta hanyar shiga yin sulhu da 'yan bindiga ba tare da saninta ba. Mannir Haidar Kaura da ke zama kwamishinan watsa labarai na gwamnatin jihar Zamfara ya ce: " Kwatsam muka ji gwamnatin tarayya ta aiko da wasu mutane da suka shiga cikin daji suna sulhu da 'yan bindiga masu kashe mutane . Mu dama gwamnatin jiharmu karkashin Dr Dauda mun ce ba za mu yi sulhu da 'yan bindiga ba saboda a baya gwamnatocin da suka gabata sun yi amma sulhun bai yi tasiri ba."

Karin haskeTasirin yaki da 'yan bindiga a jihar Zamfara

Matsalar tsaro ta dade tana addabar gwamnatocin da suka shude a Zamfara da Katsina

A nasu bangaren masana tsaro irin su Shehu Ladan Army na ganin cewar matikar babu hadin Kai tsakanin mahukuntan biyu,  babu ranar karewar matsalar tsaro, kuma duk abin da gwamnatin tarayya za ta yi dole ne ta tuntubi jiha. Ya ce: " Ya kamata gwamnatin tarayya ta gaya wa gwamnatin jihar Zamfara cewa za mu shigo domin a samu hadin Kai a hada karfi da karfe. Amma a ce gwamnatin jiha na kokarin samar da hanyoyi da take ganin sun dace, sannan kuma ace gwamnatin tarayya ta ware za ta yi sulhu da 'yan bindiga, ba za ta yake su ba"

Karin haske:Najeriya: Jihar Zamfara ta dauki sabbin matakai da nufin magance matsalar tsaro a jihar

Barrister Bulama Bukarti mai bincike kan harkokin tsaro a nahiyar Afrika ya ce al'ummar da hare-haren 'yan bindigar ya shafa a  garuruwa a Zamfara ma na bukatar aji ra'ayinsu kafin duk mataki na sulhu da 'yan bindiga balle gwamnatin jiha da ke da hakin lura da kai-kawo a jihar Zamfara.Ya ce: "Abu na farko shi ne a tattauna da al'ummar da hare-haren 'yan bindigar ya daidaita don jin ko sun yarda a yi sulhu da wadanan mutanen, domin idan matan da aka ci zarafinsu da wadanda aka cutar ba su amince ba duk kokarin sulhu da aka yi ba zai yiwu ba. Sannun a duba al'ummar da abin ya daidaita a tallafa ma rayuwarsu"  

Al'ummar jihar Zamfara na ci gaba da jin radadin hare-haren 'yan bindigaHoto: Str/Getty Images/AFP

Sai dai a wata sanarwar ta ministan watsa labaran Najeriya ya fitar Alhaji Mohammed Idris ta misanta hannu gwamnatin tarayya da sulhu da 'yan bindigar a jihar Zamfara. Ministan ya zargi gwamnan da siyasantar da matsalar tsaro, inda bangaren gwamnan shi ma ya musanta zargin.