1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnati ta ja kunnen 'yan IPOB kan zaben Anambra

October 26, 2021

Kasa da tsawon makonni biyu kafin a gudanar da shi, bisa dukkan alamu makomar zaben gwamnan jihar Anambra na shirin zaman zakaran gwajin dafi ga tarrayar Najeriya da ke fuskantar zabukan kasar cikin halin rudu.

Nigeria pro-Donald-Trump-Kundgebung der Indigenous People of Biafra in Port Harcourt
Hoto: Getty Images/AFP

An ja daga a tsakanin matasan IPOB da ke fatan nasarar hana zaben jihar Anambra da suka aike da sako a kokarin cika burin ballewa, da kuma mahukuntan Najeriya da ke kallon zaben a matsayin kokarin sake mai da fatalwar Biafra zuwa kabarinta. Kuma daga dukkan alamu bangarorin guda biyu na karin azamar cika burin mai tasiri ga makoma ta kasar anan gaba.

Wata sanarwar mahukuntan tarrayar Najeriyar suka fitar ta yi gargadi ga masu awaren cewar Abujar na da karfin hatsin da take shirin turawa zuwa Anambra da nufin samun nasarar zaben, a fadar Maigari Din Gyadi da ke zaman ministan 'yan sandan tarrayar Najeriya.

Gwamnati na son amfani da 'yan sanda wajen gudanar da zaben jihar AnambraHoto: Olamikan Gbemiga/AP Photo/picture alliance

Ya zuwa yanzu dai akalla jami'an 'yan sanda dubu 34 da suka hada da kwamishonin 'yan sanda 14 ne fadar mulki ta Abuja ta ce tana shirin turawa sako da lungunan jihar Anambra da nufin tauna tsakuwa a cikin neman tsorata aya. Sai dai in har 'yan sandan na da burin tsorata masu kayar bayan dai, tuni 'ya'yan kungiyar IPOB sun yinasarar tsorata turawan zaben da masu ruwa da tsaki a aikin zaben.

 

Wasu matasan Arewa na son a bar 'yan Biafra su balle

Majiyoyi a jihar Anambra sun ce tsoron IPOB na tilasa direbobi kin jigilar kayan zabenen. Sai dai kuma gwamnatin tarayyar Najeriyar na jan kunnen kau da kai a bangare na kasashen waje da Abujar ta ce su koma 'yan kallo cikin siyasar kasar. 

A bar masu neman ballewa su cika burinsu, in ji kungiyoyin matasan arewacin NajeriyaHoto: Getty Images/AFP

Shugaba Buhari bai boye wa jakadun kasashen duniya irin rudu na siyasar tarrayar Najeriyar ba , haka bai boye bukatar su na kallo daga nesa cikin rukuki na siyasa ta kasar ba. Sai dai a yayin da dattawan kasar suke shirin tauna tsakuwa, a wani abun da ke zama na ba zata matasan arewacin kasar sun nufi kotu da nufin neman kyale 'yan rajin Biafran su balle a cikin ruwan sanyi.

Abdul'azeez Sulaiman na zaman kakakin gamin gambizar kungiyoyin matasan arewacin kasar CNG, kuma ya ce sun je kotun ne da nufin taimaka wa masu neman ballewa cika burinsu.