Kungiyar NLC ta janye yajin aiki
November 16, 2023Babban abin da ya fi damun al'ummar Najeriyar sakamakon yajin aikin gama gari na kungiyoyin kwadagon dai, shi ne batun katse hasken wutar lantarki da hana bankuna aiki. An samu cimma maslaha ne a kan wannan yajin aiki bayan dauki ba dadi da ma zargin juna a tsakanin gwamnatin Najeriyar da kungiyoyin kwadagon kasar na NLC da TUC, abin da ya kai ga zuwa kotu. Sai dai hakan bai yi tasiri ba, inda aka sake komawa teburin sulhu bisa lallashi da ban baki daga bangaren gwamnatin Najeriyar. Mai bai wa shugaban Najeriya shawara a fannin tsaro Mallam Nuhu Ribadu da ya shige gaba a bangaren gwamnati ne ya samu shawo kan 'yan kwadagon, inda suka amince da shan ruwa mai sanyi don dakatar da shan yajin mai dankaren zafi da suka sha.
Yajin aikin na kwanaki biyu ya gurgunta al'ammura da dama a Najeriyar, kama daga hasken wutar lantarki da bankuna da ma wasu gidajen man fetir da suka rufe. Sai dai ba kamar lokutan baya ba 'yan Najeriyar da ma wasu ma'aikatan sun yiwa kungiyar tutsu a wannan karon, inda suka ci gaba da gudanar da harkokinsu. Tuni dai al'ammura suka fara dawowa yadda suke a Najeriyar, kama daga samun hasken wutar lantarki zuwa ga bankuna da ma ma'aikatun gwamnati. Murna har ciki ga mafi yawan 'yan Najeriyar, wadanda suka dogara da fita kafin samun abin da za su ci a ma gudanar da harkokinsu na yau da kullum. Yajin aiki dai na neman zama dan kullum a Najeriyar da matsaloli na koma bayan tattalain arziki suka addabi al'ummarta, kana matsalar rashin tsaro ta kara ta'azzara halin da ake ciki.